Amnesty Ta Soki Yadda Ake Take Hakkokin Dan'adam A Kasar Masar
Kungiyar kare hakkin dan 'adam ta kasa da kasa Amnesty International ta soki yadda ake hana mutanen Masar tofa albarkacin bakinsu
Kungiyar ta siffata abin da yake faru a Masar na daure masu bayyana ra'ayinsu akan mulkin Abdulfattah al-sisy da cewa; Kasar ta zama kamar kurkuku.
Rahoton da kungiyar ta kasa da kasa ta fitar ya bayyana cewa; Daga watan Disamba zuwa yanzu an kame mutane 111 saboda sun bayyana ra'ayinsu akan salon mulkin Abdulfattah al-sisy, wanda ya fi dukkanin mutanen da aka taba kamawa a tsawon mulkin Husni Mubarak saboda irin wannan dalilin.
Manajar kungiyar ta Amnesty International mai kula da yankin arewacin Afirka Najiyah Bu Na'im ta ce; A halin yanzu bayyana ra'ayi akan gwamnatin Masar wani abu ne mai matukar hatsari fiye da kowane lokaci a baya, domin ana daukar wanda ya yi hakan ko da ta ruwan sanyi ne a matsayin mai laifi.
Gwamnatin Abdulfattah al-sisy tana daukar duk wani mai sukar gwmanatin a matsatin dan ta'adda.
Kawo ya zuwa yanzu da akwai mutane 65,000 da ake tsare da su a gidan kurkuku.