Takaitacen Tarihin Shugaba Mahamadu Isufu Na Nijar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3337-takaitacen_tarihin_shugaba_mahamadu_isufu_na_nijar
A Ranar 2 ga watan Afrilun nan ne aka rantsar da Alh. Mahamadou Issoufou a wani wa’adin shugabancin kasar Nijar na biyu bayan ya lashe zaben kasar zagaye na biyu da ‘yan adawa suka kauracema a ranar 20 ga watan Maris.
(last modified 2018-08-22T06:58:04+00:00 )
Apr 03, 2016 11:21 UTC

A Ranar 2 ga watan Afrilun nan ne aka rantsar da Alh. Mahamadou Issoufou a wani wa’adin shugabancin kasar Nijar na biyu bayan ya lashe zaben kasar zagaye na biyu da ‘yan adawa suka kauracema a ranar 20 ga watan Maris.

A cikin jawabin daya gabatar bayan rantsar da shi Isufu ya jaddadda cewa zai mayar da hankali wajen yaki da ta’addanci tare da kokarin magance wasu matsalolin ‘yan kasar, dama wadanda suka dabaibaye tafiyar kasar dake cikin kasashen da ake yiwa kyallon mafi talauci a duniya.

Sashen hausa na radiyo Iran ya kawo muku kadan daga cikin tarihin shugaban

An dai haifi Mahamadou Isufu a 1951 a garin Dan Daji dake Illela a jihar Tahoua

Ya kuma karanta fannin ilimin hako ma'adanai a birnin Saint Etienne na Faransa inda ya samu digirin Injiniya a 1979.

Bayan ya koma gida, Mahamadou Isufu ya rike manyan mukamai daban-daban da suka hada da Direktan sashen ma'adanai a Ma'aikatar ma'adanai da masana'antu daga 1980 zuwa 1985 da kuma Babban Sakataren kamfanin hako Uranium na Somair da ke Arlit daga 1985 har ma ya rike mukamin Darekta a 1991 zuwa 1992.

Tun da Nijar ta koma kan tafarkin Demokradiyya a 1993, Mahamadou Issoufou ya tsaya takarar shugabancin kasa a kowanne zaben da aka yi.

Ya jagoranci jam'iyyar PNDS-Tarayya tun daga lokacin da aka kafa ta a shekarar 1990 har zuwa lokacin da ya hau kan karagar mulki a 2011.

Kafin ya zama shugaban kasa, Mahamadou Issoufou ya rike manyan mukaman siyasa da suka hada da Firaminista daga 1994 zuwa 1995 da shugaban majalisar dokoki daga 1995 zuwa 1996.

Daga 1999 har zuwa 2010, ya kasance dan majalisar dokokin kasar, kuma shi ne madugun 'yan adawa.

A watan Nuwamba na 2015 ne, jam'iyyar PNDS-Tarayya ta tsaida shugaba Mahamadou Issoufou a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasa zagaye na farko da aka gudanar a ranar 21 ga watan Fabrairu, kuma ya lashe zaben da kashi sama da 48%, saidai hakan bai bashi damar lashe zaben ba tun zagayen farko, kamar yadda yayi ta ikirari a yakkin neman zaben sa.

Hakan ne kuma yasa aka je zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a ranar 20 ga watan Maris daya gabata inda ya lashe zaben da ‘yan adawa suka kauracewa da kashi sama da 92%.

A cikin jawabin daya gabatar bayan rantsar da shi Isufu ya jaddadda cewa zai mayar da hankali wajen yaki da ta’addanci tare da kokarin magance wasu matsalolin ‘yan kasar, dama wadanda suka dabaibaye tafiyar kasar dake cikin kasashen da ake yiwa kyallon mafi talauci a duniya.

Alh. Mahamadu Isufu wanda akewa ikirari da ‘’ Zaki’’ Yana da mata 2 da kuma 'ya'ya 4.