Burundi Ta Dakatar Da Ayyukan Dukkan Kungiyoyin Agaji Masu Zaman Kansu
Gwamnatin kasar Burundi Ta Dakatar da ayyukan dukkan kungiyoyin bada agaji na kasashen waje wadanda suke aiki a cikin kasar.
Kamfanin dillanin labaran Anatolio ya nakalto majiyar fadar shugaban kasar Burundi tana fadar haka a yau Asabar ta kuma kasar da cewa ta dau wannan matakin ne don kungiyoyin basa kiyaye dokoki da sharuddan da gwamnatin kasar ta shimfida masu na gudanar da ayyukansu a kasar.
Labarin ya kara da cewa majalisar tsaron kasar Burundi karkashin jagorancin shugaban Pierre Nkrurunziza ta ce ta dakatar da su ne na tsawon watanni ukku kuma a cikin wannan lokacin gwamnatin zata yi binciken ayyukan kungoyoyin don gano inda suke sabawa sharuddan da aka shimfida masu.
Kafin wannan matakin dai kasashen turai sun dakatar da tallafin kudaden da suke bawa kasar Burundi kai tsaye, don haka ne gwamnatin Pierre Nkuruziza take son karfafa ikonta a kan kudaden da kungiyoyin bada agaji suke shigo da su kasar don sune kadai suke shigo da kudaden kasashen waje kasar.