Masar : An Zargi Tsohuwar Gwamnatin Mubarak Da Kashe-Kashen Gilla
Dan tsohon shugaban Majalisar Dokokin Masar ya zargi tsohuwar gwamnatin kasar karkashin shugabancin Husni Mubarak da aiwatar da kashe-kashen gilla kan masu sabanin ra'ayi da ita.
Jaridar Ra'ayul-Yaum ta watsa labarin cewa: Ayman Rifa'at Al-Mahjub ya bayyana cewa: Wasu manyan jami'an tsohuwar hambararriyar gwamnatin Husni Mubarak suna da hannu dumu-dumu a aiwatar da kisan gilla kan mahaifinsa Rifa'at Al-Mahjub.
Ayman ya kara da cewa: A lokacin da suka yunkuro domin neman hakkinsu kan kashe mahaifinsa, Zakariyya Azmi shugaban ofishin fadar shugaban kasa a zamanin mulkin Husni Mubarak ya gargade shi tare da yi masa barazanar cewa matukar yana son ci gaba da rayuwa, to dole ne ya janye daga kan maganar tare da yin shiru.
Tun a ranar 12 ga watan Oktoban shekara ta 1990 ne aka aiwatar da kisan gilla kan Rifa'at Al-Mahjub a kan babbar hanyar birnin Alkahira na kasar Masar, kuma har yanzu babu wani bayani da ya fito daga jami'an tsaron kasar kan batun.