Afirka Ta Tsakiya: Fadace-fadace Sun Ci Rayukan Mutane 30
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da kashe mutane 30 a cikin watanni biyu na bayan nan a kasar Afirka ta tsakiya.
Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ya ambato majiyar Majalisar Dinkin Duniya a kasar Afirka ta tsakiya tana cewa; A cikin watannin Agusta da Satumba na wannan shekarar ta 2018 da ake ciki, kungiyoyin da suke dauke da makamai a kasar sun kashe mutanen a gundumar Haute-Kotto.
Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya kuma bayyana cewa; Fadace-fadace da ake yi a cikin kasar sune ummul haba'isin hijirar mutane dubu 32 a cikin fadin kasar.
Rundunar Malajisar Dinkin Duniya a kasar ta Afirka ta tsakiya da ake kira; Minuska, ta yi tir da hare-haren da ake kai wa a fadin kasar wadanda suke haddasa asarar rayuka da barnata dukiya.