Afirka Ta Tsakiya: Fadace-fadace Sun Ci Rayukan Mutane 30
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33649-afirka_ta_tsakiya_fadace_fadace_sun_ci_rayukan_mutane_30
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da kashe mutane 30 a cikin watanni biyu na bayan nan a kasar Afirka ta tsakiya.
(last modified 2018-10-16T12:11:31+00:00 )
Oct 16, 2018 12:11 UTC
  • Afirka Ta Tsakiya: Fadace-fadace Sun Ci Rayukan Mutane 30

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da kashe mutane 30 a cikin watanni biyu na bayan nan a kasar Afirka ta tsakiya.

Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ya ambato majiyar Majalisar Dinkin Duniya a kasar Afirka ta tsakiya tana cewa; A cikin watannin Agusta da Satumba na wannan shekarar ta 2018 da ake ciki, kungiyoyin da suke dauke da makamai a kasar sun kashe mutanen a gundumar Haute-Kotto.

Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya kuma bayyana cewa; Fadace-fadace da ake yi a cikin kasar sune ummul haba'isin hijirar mutane dubu 32 a cikin fadin kasar.

Rundunar Malajisar Dinkin Duniya a kasar ta Afirka ta tsakiya da ake kira; Minuska, ta yi tir da hare-haren da ake kai wa a fadin kasar wadanda suke haddasa asarar rayuka da barnata dukiya.