Karon Farko Mace Ta Zama Shugabar Kasa A Habasha
(last modified Thu, 25 Oct 2018 19:05:07 GMT )
Oct 25, 2018 19:05 UTC
  • Karon Farko Mace Ta Zama Shugabar Kasa A Habasha

Yan majalisar dokokin kasar Habasha sun zabe macce ta farko a matsayin shugabar kasar.

Majiyar gwamnatin kasar Habasha ta bayyana cewa daga cikin yan majalisar dokoki 546 da take da su, yan  majalisa 487 ne suka sami halattar zaman majalisar a yau Alhamis, inda suka zabi Sahle warq Zeyude a matsayin sabon shugaban kasa. 

Da wannan kuma Sahle Warq ta zama shugaban kasar habasha na hudu tun bayan an yi wa kundin tsarin mulkin kasar koskorima a shekara 1995, kuma iata ce macce ta farko wacce ta taba zama hawa kan kurar shugaban kasa. 

Tsohon shugaban kasar Habasha da ya sauka Mulatu Teshome ya rike muamin shugaban kasar Habasha tun shekara 2013. A cikin kundin tsarin mulkin kasar Habasha dai shugaban kasa yana iya rike wannan mukamin na tsawon shekaru 6 har sau biyu. 

Kafin zaben Sahle Warq dai ta yi ayyukan diblomasiyya da dama ta kuma taba zama wakilin babban sakataren MDD Antonio Gotterest a tarayyar Afrika