Masar : Kotu Ta Sanya Sunaye Wasu 'Yan Ihwan Cikin Jerin 'Yan Ta'adda
Wata kotu a birnin Alkahira na kasar Masar ta sanya sunayen 'yan kungiyar Ihwanul-Muslimin 164 cikin jerin sunayen 'yan ta'adda a kasar.
Wata kotu a birnin Alkahira na kasar Masar a yayin zamanta a jiya Lahadi ta sanar da cewa: A karkashin shirin yaki da ta'addanci a Masar akwai wasu 'yan kungiyar Ihawanul-Muslimin ta 'yan uwa musulmi a kasar da suke barazana ga al'ummar Masar da 'yancinsu gami da kokarin tauyaye musu hakkokinsu, sakamakon haka kotun ta zartar da hukuncin sanya sunayensu cikin jerin gungun 'yan ta'adda a kasar.
Daga cikin 'yan kungiyar ta Ihwan 164 da aka sanya cikin jerin 'yan ta'addan har da wasu daga cikin shugabannin kungiyar ta Ihwan misalin Muhammad Islambuli, Tariq Al-Zamra, Asim Abdul-Majid, Majdi Husaini da kuma Asim Dayab.