'Yan Adawa Sun Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zanga A Nijer
Gungun jam'iyun 'yan adawa a jamhiriyar Nijer sun gudanar da gagarumar zanga-zangar nuna adawa da kundin zaben kasar
A jiya Lahadi ne, dubban jama'a suka fito a birnin Yamai domin amsa kiran 'yan dawa wajen nuna adawarsu da kundin zaben kasar ta Nijar da suke zargin bangaran gwamnati da shirya manakisa a game da zaben.
Tsohon shugaban kasar ta Jamhuriyar Nijar Alhaji Mahamane Ousmane ,shi ne ya jagorancin zanga-zanga , inda wasu ke ganin cewa ba'a taba ganin irinta ba daga cikin jerin zanga-zangar da 'yan adawan ke shiryawa a birnin na Yamai.
'Yan adawar na ganin kudiri ne dai mai lamba takwas na kundin zaben kasar ta Jamhuriyar Nijar shi ne ya haddasa cecekuce a kasar.
Wannan kudiri kuma ka iya haramta wa madugun 'yan adawan kasar Hama Amadou tsayawa takara a zabukan kasar masu zuwa abin da 'yan adawar na Nijar ke ganin cewa ba za su aminci da hakan ba.