Masar: za a Koma Tattaunawa Kan batun Madatsar Ruwa Ta Al-nahdah
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34153-masar_za_a_koma_tattaunawa_kan_batun_madatsar_ruwa_ta_al_nahdah
Mahukuntan kasar masar sun sanar da cewa za a koma kan teburin tattaunawa tsakanin Masar da Habasha kan batun madatsar ruwa ta Al-nahdah.
(last modified 2018-11-19T13:05:01+00:00 )
Nov 19, 2018 13:05 UTC
  • Masar: za a Koma Tattaunawa Kan batun Madatsar Ruwa Ta Al-nahdah

Mahukuntan kasar masar sun sanar da cewa za a koma kan teburin tattaunawa tsakanin Masar da Habasha kan batun madatsar ruwa ta Al-nahdah.

Kamfanin dillancin labaran Sputnik ya bayar da rahoton cewa, Mustafa Madbuli firayi ministan kasar Masar ya sanar da cewa, sun cimma matsaya tare da takwaransa na Habasha Abi Ahmad kan cewa, bangarorin biyu za su koma kan teburin tattaunawa kan batun madatsar Nahdah.

Firayi ministan an masar ya ce, tatatunawar za ta mayar da hankali kan muhimman batutuwa wadabnda ba a cimma matsaya a kansu tsakanin bangarotin ba a lokutan baya.