An Ci Tarar kamfanonin Sadarwa Na Wayar Salula A Ghana
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34203-an_ci_tarar_kamfanonin_sadarwa_na_wayar_salula_a_ghana
Hukumar kuda harkokin sadarwa ta kasar Ghana ta ci tarar wasu kamfanonin sadarwa na wayar salula, Dala Miliyan bakwai saboda kasawa wajen biyan bukatun al'umma.
(last modified 2018-11-23T04:47:11+00:00 )
Nov 23, 2018 04:47 UTC
  • An Ci Tarar kamfanonin Sadarwa Na Wayar Salula A Ghana

Hukumar kuda harkokin sadarwa ta kasar Ghana ta ci tarar wasu kamfanonin sadarwa na wayar salula, Dala Miliyan bakwai saboda kasawa wajen biyan bukatun al'umma.

Kamfanonin da aka ci tarar sun hada da Mobile, Vodafone, MTN, GLO da kuma Airtel, saboda rashin bada sabis ko hanyoyin sadarwa na wayar hannu masu inganci ga abokanin cinikinsu.

Matsalar rashin samun hanyar sadarwar mai kyau ta fi kamari ne ga mutanen dake rayuwa a kauyuka.

Bayanai sun nuna cewa a wasu kauyukan sai mutane sun hau kan bishiyoyi ko kuma suyi tafiya mai nisa da kafa domin samun sabis wanda zai basu damar kira ko samun kira da wayoyuin hannunsu.