Masar : An Yanke Wa Mutum 9 Hukuncin Kisa, Kan Kashe Babban Alkali
(last modified Sun, 25 Nov 2018 16:21:05 GMT )
Nov 25, 2018 16:21 UTC
  • Masar : An Yanke Wa Mutum 9 Hukuncin Kisa, Kan Kashe Babban Alkali

Wata kotu a Masar ta tabbatar da hukuncin kisa ga mutum tara da aka samu da laifin kisan mai shigar da kara na gwamnatin kasar a cikin shekara 2015 a birnin Alkahira.

A cikin shekara 2017 ne wata kotun kasar ta yanke irin wannan hukuncin ga mutum 28 da ake zargi da kashe babban alkalin, mai suna Hicham Barakat a wani harin bam da aka kai wa ayarin motarsa a babban birnin kasar.  

A yanzu dai mutanen basu da hurumin daukaka wata kara, kamar yadda wata majiyar shari'a ta tabbatar wa da kamfanin dilancin labaren AFP.

Tun dai lokacin babu wata kungiya data alhakin kai harin kan babban maio shigar da kara na kasar, saidai biyo bayan harin 'yan sandan kasar sun sanar da cafke mambobin kungiyar nan ta 'yan uwa musulmi.