Nijar : An Fara Gasar Kokowar Gargajiya Karo Na 40
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34570-nijar_an_fara_gasar_kokowar_gargajiya_karo_na_40
A Jamhuriya Nijar, da yammacin yau ne aka bude gasar kokowar gargajiya ta kasar karo na 40 da jihar Tillaberi ke karbar bakunci a bana.
(last modified 2018-12-25T17:19:17+00:00 )
Dec 25, 2018 17:19 UTC
  • A shekara 1975 ne lokacin mulkin tsohon shugaban kasar mirigayi Seyni Kountché, aka kirkiro da wannan gasar ko kwampala a matkin hada kan al'ummar kasar.
    A shekara 1975 ne lokacin mulkin tsohon shugaban kasar mirigayi Seyni Kountché, aka kirkiro da wannan gasar ko kwampala a matkin hada kan al'ummar kasar.

A Jamhuriya Nijar, da yammacin yau ne aka bude gasar kokowar gargajiya ta kasar karo na 40 da jihar Tillaberi ke karbar bakunci a bana.

'Yan kokowa 80 ne daga jihohin kasar takwas ne zasu fafata a gasar da za'a kwashe kusan kwanaki goma anayi domin fidda zakara.

A bara dai dan kokowa Tassiu Sani ne daga jihar Zinder ya dauki takobin, wanda a yau ya mika shi ga ministan wassani da matasa na kasar, a matsayin bude gasar ta bana.

A shekara 1975 ne lokacin mulkin tsohon shugaban kasar mirigayi Seyni Kountché, aka kirkiro da wannan gasar ko kwampala a matkin hada kan al'ummar kasar.

Duk da hakan gasar dai na da farin jini sosai, sannan tana samun karbuwa ga jama'ar kasar harma dana ketare.