Komitin Tsaro Na MDD Na Sanaya Ido A Zaben Kongo Kinshasa
(last modified Sat, 05 Jan 2019 07:01:04 GMT )
Jan 05, 2019 07:01 UTC
  • Komitin Tsaro Na MDD Na Sanaya Ido A Zaben Kongo Kinshasa

Komitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya bada sanarwan cewa yana sanya ido a kan yadda ake gudanar da kidayar kuri'u na zaben shugaban kasa wanda aka gudanar a kasar Democradiyyar Congo

Kamfanin dillancin labaran NAN na Najeriya ya nakalto jakadan kasar Faransa a majalisar dinkin duniya yana fadar haka a jiya Jumma'a. Ya kuma kara da cewa komitin ya gudanar da zama a asirce don tattauna batun zaben na Kongo, amma bai bada sanarwan hadin  guiwa a halin yanzu ba. 

Jakadan kasar ta Faransa a MDD Francois Delattre ya fadawa yan jaridu cewa komitin yana bukatar sakamakon zaben ya yi dai-dai da abinda mutanen kasar suka zama. 

Francois Delattre ya ce ana saran wannan zaben shi ne zai zama zabe na farko wanda za'a mika mulki ga wata gwamnati a kasar ta Kongo a cikin ruwan sanyi tun bayan samun 'yencin kan kasar a shekara 1960 .

Kafin haka dai Chocin catholica ta kasar ta bukaci hukumar zaben ta bada sakamako dai-dai da kuri'un mutane don ita ta san wanda ya lashe zaben.

Amma jam'iyya mai mulkin kasar ta yi watsi da kiran chocin, ta kuma kara da cewa cocin bai kamata ya fadi haka ba, don bisa dokokin tsarin mulkin kasar ba wanda yake da alhakin bayyana sakamakon zaben sai hukumar zabe. 

A gobe Lahadi ne ake saran sakamakon zaben na wucin gadi zai fara fita.