An Tsaurara Matakan Tsaro A Masar
A yayin da ake shirye-shiryen gudanar da bikin zagawoyar cika shekaru takwas da juyin juya halin kasar wanda ya kawo karshen gwamnatin kama karya ta Hosni Mubarak, gwamnatin kasar Masar ta tsaurara matakan tsaro a manyan hanyoyi da wuraren taruwar Al'ummar kasar
Tashar talabijin din Al-alam dake watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta nakalto Namir Arrafa'i kakakin Rundunar tsaron kasar Masar a daren jiya Laraba na cewa wannan matakin tsaro da aka dauka, da nufin tabbatar da tsaro ne a yayin bikin zagawoyar juyin juya hali na ranar 25 ga watan janairu.
A gobe juma'a 25 ga watan Janairu, al'ummar kasar Masar ke gudanar da bikin juyin juya hali karo na takwas wanda ya kawo karshen gwamnatin tsohon shugaban kasar dan milkin kama karya Hosni Mubarak a shekarar 2011.
Duk da irin wannan matakan tsaron da gwamnati ta dauka, babu wata kungiya ko gungu da suka kira zanga-zanga ko jerin gwano a kasar.
Bayan kwashe shekaru takwas da juyin juya halin kasar, wasu Misrawa na ganin cewa babu wani abu daya da ya tabbata, wanda aka juyin domin shi, domin har ya zuwa yanzu, da dama daga cikin al'ummar kasar na fama da matsalar rashin aikin yi, ga kuma hauhawar farashi na kayan masrufi, bugo da kari ga matsalar rashin tsaro da kasar take fama da shi.