Masar : Wasu 'Yan Majalisa Sun Bukaci Al'Sisi Ya Yi Tazarce
(last modified Mon, 04 Feb 2019 03:41:06 GMT )
Feb 04, 2019 03:41 UTC
  • Masar : Wasu 'Yan Majalisa Sun Bukaci Al'Sisi Ya Yi Tazarce

Wasu 'yan majalisar dokoki a Masar, sun gabatar da wani kudiri dake neman a yi gyaren fuska wa kundin tsarin mulkin kasar, ta yadda shugaba Abdel Fattah Al Sisi ya sake tsayawa takara shugaban kasa bayan wa'addin mulkinsa na biyu a shekara 2022.

Kudirin da kashi guda cikin biyar na 'yan majalisar dokokin suka gabatar wa shugaban majalisar, ya tanadi bukatar yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya hada da shekarun wa'adin mulki na shugaban kasa wanda yake a shekaru hudu-hudu har sau biyu.

'Yan majalisar 120 cikin 596 na bukatar a yi gyaren fuska wa kundin ta yadda wa'adin mulki zai kasance shekaru shida-shida har sau biyu, wanda kuma a cewarsu zai baiwa shugaba Al-Sisi damar sake tsayawa takara kuma a zaben shugaban kasar sau biyu bayan karshen wa'adinsa na biyu a shekara 2022.

'Yan majalisar da suka gabatar da bukatar sun hada dana bangaren kawancen jam'iyyu masu rinjaye a majalisar da kuma na 'yan indifanda. 

To saidai akwai bukatar a gudanar da zaben raba gardana Idan har majalisar ta amince da bukatar.