Feb 04, 2019 04:48 UTC
  • Amurka Ta Tsananta Kai Hare Hare kan Al'Shabab A Somaliya

Amurka ta tsananta kai hare harenta kan mayakan al'shabab a Somaliya a baya bayan nan, inda ta hallaka talatin daga cikinsu a karshen makon jiya, a tsakiyar kasar a kusa da Mogadisho babban birnin Somaliya.

Hare hare na zuwa ne duk da ikirarin shugaban kasar ta Amurka na cewa, kasarsa ba zata zame wa duniya rundinar tsaro ba.

Bayanai sun nuna cewa Amurka ta kai hare haren sama har sau goma kan mayakan al'shabab a Somaliya tun farkon wannan shekara, wanda kuma a bara ta kai hare haren sama hamsin ne.

Amurka dai ta ce tana kai hare haren ne domin karya laggon kungiyar ta Al'shabab a Somaliya domin kada mayakan sun maida kasar sansani na kisa kai hare haren ta'addanci a kasashen yamma.

Kungiyar al'shabab dai na daga cikin kungiyoyin masu tsatsauran ra'ayi dake zama babbar barazana a yankin kahon Afrika.

Tags