Feb 14, 2019 19:16 UTC
  • Majalisar Dokokin Kasar Masar Ta Amince Da Batun Tsawaita Shugabancin Shugaban Kasar

Majalisar dokokin kasar Masar ta fara aikin tattauna batun gudanar da gyara wa kundin tsarin mulkin kasar wanda zai bawa shugaba Abdulfattaha Assisi damar shugabancin kasar har zuwa shekara ta 2034.

Tashar talabijin ta Almayadeen a kasar Lebanon ta bayyana cewa a wannan karon majalisar ta amince da fara batun sauya doka ta tsawon shekarun da shugaban kasa zai yi a duk lokacinda aka zabe shi daga shekaru 4 zuwa 6 a cikin kundin tsarin mulkin kasar.

Labarin ya kara da cewa idan wannan sauyin ya tabbata shugaba Abdulfattah Assisi yana iya ci gaba da shugabancin kasar har zuwa shekara ta 2034, wato har zuwa shekaru 15 masu zuwa. 

Janar Abdul Fattaha Assisi ya hau kan kujerar shugabancin kasar Masar ne bayan juyin mulkin da yayi wa zabebben shugaban kasar ta Masar Mohammad Mursi a sheklara ta 2013, sannan ana sake zabensa a matsayin shugaban kasa karo na biyu a shekara ta 2018 da ta gabata. 

A bisa kundin tsarin mulkin kasar masar na yanzu dai shugaban bai isa ya tsaya takara shugaban kasa a karo na ukku ba. 

Tags