Feb 19, 2019 12:23 UTC
  • Masar: An Kai Harin Ta'addanci A Birnin Alkahira

Harin ta'addancin ya yi sanadiyyar mutuwar jami'an tsaro 3 da kuma jikkata wasu ukun

Kafafen watsa labarun kasar Masar sun ce; Bom din ya tashi ne a kusa da masallacin Azhar dake birnin na al-kahira a gundumar al-jamaliyyah

Majiyar tsaron Masar ta kuma lamarin ya faru ne a daidai lokacin da jami'an tsaron suke bin sawun wani dan ta'adda sannan kuma su ka killace shi. Dan ta'addar ya tashi bom din ne domin ya samu ya gudu.

Kasar Masar tana fama da matsalar tsaro saboda hare-haren da 'yan ta'adda suke kai wa a sassa daban-daban na kasar.

A yankin Sina mai iyaka da Palasdinu da akwai kungiyoyi irin su Da'esh da kuma al'ka'ida. 

Tags