An gudanar da zanga-zanga a kasar Ghana
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3529-an_gudanar_da_zanga_zanga_a_kasar_ghana
Wasu kungiyoyin fararen hula sun gudanar da zanga-zangar kalu balantar hukumar zabe a kasar Ghana
(last modified 2018-08-22T11:28:05+00:00 )
Apr 07, 2016 08:43 UTC
  • An gudanar da zanga-zanga a kasar Ghana

Wasu kungiyoyin fararen hula sun gudanar da zanga-zangar kalu balantar hukumar zabe a kasar Ghana

Dubun dubatan 'yan kasar Ghana ne suka gudanar da jerin gwano a birnin Kumasi dake jihar Ashanti, domin neman gudanar da gyara da hukumar zaben kasar

Mahalarta zanga-zangar sun bayyana cewa matukar ba a gudanar da gyran ba tare kuma mutunta dokokin kasar , za su ci gaba da zanga-zangar a fadin kasar baki daya.

Wannan zanga-zanga na zuwa ne a yayin da kasar ke shirye shiryen gudanar da zabe na shekarar 2016.