Masar: An Zartar Da Hukuncin Kisa Akan Wasu Mutane
Kafafen watsa labarun Masar sun ce an zatar da hukuncin kisa akan mutane 9 wadanda aka samu da laifi wajen kai wa babban mai shigar da kara na kasar hari
Kamfanin dillancin Labarun Jamus ya ba da labarin cewa; Gwamnatin Masar ta zartar da hukuncin kisan akan mutanen 9 duk da cewa kungiyar kare hakkin bil'adama ta "Amnesty Internaional" ta yi kira da ka da a kashe mutanen
A cikin watan Yuni na 2015 ne dai aka kai wa babban shigar da kara na kasar hari da wata mota da aka makare da bama-bamai, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa
Tare da cewa kungiyar Ikhwanul-Muslimin ta nesanta kanta daga kisan, sai dai jami'an tsaro sun kame da dama daga cikin 'ya'yanta
A shekarar 2018 da ta gabata ne dai kotun daukaka kara a Masar ta tabbatar da hukuncin kasa akan mutanen
Sai dai kungiyar kare hakkin bil'adama ta "Amnesty International' ta bayyana cewa; Ba a yi wa mutanen shiri'a mai adalci ba, an kuma azabtar da su ne aka karbi bayanai daga gare su.