Feb 27, 2019 07:43 UTC
  • Za'ayi Ganawa Ta Biyu Tsakanin Trump Da Kim Jong-un

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya isa birnin Hanoi, babban birnin kasar Vietnam, inda nan ne zai yi ganawa ta biyu tsakaninsa da shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong-un.

Kafin hakan, fadar shugaban kasar Amurka wato White House ta sanar da cewa, shugaba Trump da shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un za su yi gajeren tattaunawa yau da dare, daga baya su ci abinci tare, sannan kuma su yi shawarwari a gobe.

Kafin shugaba Trump ya tashi zuwa birnin Hanoi, ya bayyana cewa yana fatan za a cimma sakamako kan wannan shawarwari.

A watan Yunin shekarar 2018, Trump da Kim Jong-un sun yi ganawa ta farko a kasar Singapore tare da daddale hadaddiyar sanarwa, inda suka cimma daidaito kan kafa sabuwar dangantaka tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa da kuma tsarin kiyaye zaman lafiya mai dorewa a zirin Koriya

Tags