Za A Gudanar Da Sauye-Sauye A Cikin Dokokin Zabe A Ghana
(last modified Sat, 09 Apr 2016 04:22:28 GMT )
Apr 09, 2016 04:22 UTC
  • Za A Gudanar Da Sauye-Sauye A Cikin Dokokin Zabe A Ghana

Hukumar zabe mai zaman kanta a kasar Ghana ta sanar da cewa za a gudanar da wasu sauye-sauye a cikin dokokin zaben kasar.

Kamfanin dillancin labaran Xin-huwa daga birnin Akra ya bayar da rahoton cewa, a wata sanarwa da shugaban hukumar zaben kasar ta Ghana Charlotte Osei ya bayar jiya Juma'a, ya tabbatar da cewa hukumar ta amince za ta gudanar da wasu sauye-sauye a cikin dokokinta.

Osei ya kara da cewa kotun kolin kasar ce ta bukaci da a gudanar da wadannan sauye-sauye, kamar yadda kuma wasu daga cikin jam'iyyun siyasa na kasar sun bayar da irin wannans hawara.

A ranar Alhamis da ta gabata ce dubban mutane suka gudanar da zanga-zanga a birnin Kumasi na jahar Ashnti, inda suka nuna rashin amincewa da wasu ka'idoji na hukumar zabe, tare da yin kira da canja wasu dokokin kafin lokacin gudanar da zaben shugaban kasa a cikin watan Nuwamban karshen wannan shekara.