Jakadan kasar Italiya dake birnin Alkahira ya fice daga kasar
Jakadan kasar Italiya dake birnin Alkahira ya fice daga kasar domin nuna Adawarsa ga Gwamnatin kasar na rashin ci gaba a binciken da ake yi na wani talibi dan kasar Italiya da ya rasa ransa sakamakon azabtar da shi.
Kamfanin dillancin Labaran kasar Faransa daga birnin Alkahira ya nakalto wani jami'in 'yan sanda a filin jirgin saman Alkahira da ya bukaci a sakaye sunansa na cewa a yau Lahadi Jakadan kasar Italiya Maurizio Massari ya bar birnin, inda ya nufi birnin Rom fadar milkin kasar Italiyan.majiyar Diplomasiyar kasar Italiyan dake birnin Alkahira ta tabbatar da wannan Labari.
A kwanakin baya dai, kasar ta Masar ta tura wata tawaga zuwa birin Rom domin tattaunawa da magabatan kasar ta Italiya kan kiisan da a ka yiwa Talibin kasar tare da daukan alkawarin gudanar da bincike domin zagulo wadanda suka aikata wannan ta'addanci, saidai magabatan na Rom sun ja hankalin tagwarorinsu na Alkahira da cewa matukar suka fahimci cewa babu wani ci gaba a binciken, za su janye jakadansu daga birnin Alkahiran.
A ranar 25 ga watan Janairun da ya gabata ne aka nemi Giulio Regeni dalibin jami'a dan kasar italiyan a binrnin Alkahiran aka rasa , bayan kwanaki 9 aka tsinci gawarsa a gefen gari, bisa bincike da masanan kiyon lafiya suka gudanar an tabbatar da cewa Regeni ya rasa ransa ne sakamakon tsananin azabar da aka yi masa.
Wannan lamari dai ya aifar da matsala a alakar dake tsakanin kasashen biyu.