An Saussauta Dokar Ta Bace A Jihar Diffa Dake Jamhuriyyar Nijer
Gwamnatin Jihar Diffa Dake Kudu Maso gabashin Jumhoriyar Nijer ta sassauta Dokar Ta Bace domin 'yan siyasa su samu damar yakin neman zabe.
Kafar watsa labaran Afirka Time ta nakalto Magajin garin Birnin Diffa Malam Hankouraou Biri-Kassoum a jiya Juma'a na cewa, bayan tattaunawar da magabatan jihar suka yi sun amince da sassauta dokar ta bace wacce aka kakabawa jihar sama da shekaru guda da suka gabata, domin baiwa 'yan saiyasa damar yakin nemen zaben shugaban kasa da na 'yan Majalisun dokako da zai gudana a ranar 21 ga wannan wata na favrayu da muke ciki.
A Ranar 29 ga watan Janairun da ya gabata Gwamnatin Jumhoriyyar Nijer ta jadadda dokar ta bace da ta sanya a jihar Diffa mai fama da rikicin Boko haram na tsahon wattani Uku, wannan dokar ta Bacen ta Baiwa jami'an tsaron kasar gudanar da bincike dare da rana da gidajen Mutane.