Nijar : Mahamadu Isoufou Ya Bayyana Kaddarorinsa
Shugaba Alh. Mahamadu Yussuf na Nijar dake shugabancin kasar a wa'adin mulki na biyu ya bayanawa kotun tsarin mulkin kasar kaddarorin daya mallaka kamar yadda dokar kasar ta tanada.
Kaddarorin da shugaban kasar ya mallaka sun tasakimanin bilyan daya da milyan dari uku na kudin CFA, kwatamcin milliyan 2,2 na dallar Amurka.
kaddarorin sun hada dana da gidaje 10 da kuma filaye a Yamai babban birnin Kasar da kuma wasu sassan kasar da suka hada da Zinder, Dongondoutchi, Tahoua, Konni, Illéla da garin Dan Daji mahaifar sa.
kazalika shugaban ya mallaki motoci ciki harda mai sulke kirar Lexus da kudin ta suka kai miliyan 100 na kudin CFA da aka saya a wannan shekara
ko baya ga hakan shugaba Isufu ya mallaki dabbobi kanana da mayan da kayan gida, da kuma asusun kudi da ba'a bayana abunda suka kunsa a kasar da kuma Faransa.
ko baya ga shugaban kasar duk mambobin gwamnatin kasar doka ta cilasta masu bayana kadarorinsu da zarar sun kama aiki, kuma hakan na kasancewa bisa doka a ko wace shakara a cikin wa'adin aikin na su.