Masar : An La'anci Al-Sisi Kan Mallakawa Saudiyya Tsibirai
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3958-masar_an_la'anci_al_sisi_kan_mallakawa_saudiyya_tsibirai
Dubban Misirawane suka gidanar wata zanga-zanga jiya Juma'a domin yin allawadai da matakin gwamnatin kasar na mallakawa Saudiyya wasu tsibiran kasar biyu.
(last modified 2018-08-22T06:58:08+00:00 )
Apr 16, 2016 06:33 UTC
  • wasu masu zanga-zanga a Masar
    wasu masu zanga-zanga a Masar

Dubban Misirawane suka gidanar wata zanga-zanga jiya Juma'a domin yin allawadai da matakin gwamnatin kasar na mallakawa Saudiyya wasu tsibiran kasar biyu.

Masu zanga-zanga da suka hada da 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi da wasu kungoyoyi na gwagwarmaya a kasar ta Masar, na bukata ga shugaban kasar Aldel fatah Al-Sisi da yayi murabus.

kazalika masu zanga-zanga dake daukeda alunna dake dauke da kalamen tofin allatsine ga mahukuntan kasar na cewa suna so duniya ta shaidi yadda cin hanci da karbar rashawa ya mamaye gwamnatin kasar su mara adalci.