An Kama Bakin Haure Kimini 100 A Kan Iyakar Niger Da Algeria
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4378-an_kama_bakin_haure_kimini_100_a_kan_iyakar_niger_da_algeria
Majiyar jami'an tsaro na kan iyaka a jumhuriyar Niger ta bayyana cewa sun kama mutane bakin haure feda 100
(last modified 2018-08-22T06:58:11+00:00 )
Apr 25, 2016 23:16 UTC
  • An Kama Bakin Haure Kimini 100 A Kan Iyakar Niger Da Algeria

Majiyar jami'an tsaro na kan iyaka a jumhuriyar Niger ta bayyana cewa sun kama mutane bakin haure feda 100

Majiyar jami'an tsaro na kan iyaka a jumhuriyar Niger ta bayyana cewa sun kama  bakin haure feye da  100 a kan iyakar kasar da Aljeria. Majiyar kungiyar The International Organisation for Migration (IOM) ta kara da cewa hakan ya auku ne a jiya litinin inda wata tashar gidan radio ta bada sanarwan cewa jami'an tsaron sun sami mata da yara kimani 122 a cikin wata mota daukar kaya guda, sannan sun kama wasu tmutane 150 kan batun.

Wasu majiyoyi sun bayyaba cewa a shekarar da ta gabata kadai bakin haure kimani duba dari ne suka tsallaka daga jihra Agasdes na arewacin kasar .

Labarin ya kara da cewa an kama mutanen ne a cikin wata motar daukan kaya a kusa da garin Assamaka, kuma an amaidasu birnin Agadest inda suke zaune a wani sananin yan gudun hijira a jihar kafin a tasa keyarsu zuwa inda suka fito.

Bakin hauren dai suna kan hanyarsu ta zuwa kasashen turai ne ta hanyar kasashen Libya, Algeria da kuma Morocco. Da dama daga cikinsu sun mutu a cikin ruwan tekun  Mededteranin sannan wasu kuma suna ta mutuwa cikin hamadar sahara  saboda kishin ruwa da rashin ambinci.