An Kashe Mai Zanga-zangar nuna kin jinin Al-Sisi
Apr 26, 2016 07:28 UTC
An Kashe Mai Zanga-zangar nun kin jinin shugaban kasar Masar Guda
Jami'an tsaro a kasar Masar sun kashe daya daga cikin masu Zanga-zangar siyasar shugaban kasar Abdulfattah al-sisy.
Rahotannin da su ke fitowa daga kasar ta Masar, sun ce wani mai zanga-zanga guda ya rasa ransa a garin Alexandaria, bayan da motar 'yan sanda mai sulke ta taka shi.
Mutanen Masar din dai suna yin Zanga-zangar ne domin nuna kin amincewarsu da mika tsibirai biyu na Tiran da Sanafir da shugaban kasar Abdulfatah al-sisy ya yi ga kasar Saudiyya.
A sassan kasar daban-daban dai an kame mutane 23 da su ke fito yin zanga-zangar.
Tags