Sama da Mutane 200 ne aka kame a Masar
Jami'an tsaron Masar sun tarwaza masu zanga-zangar adawa da baiwa kasar Saudiya tsibiran Tiran da sanafir tare da kame 237 daga cikin su
Tashar Telbijin din Al'alam dake watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta nakalto kwamishinan kare hakin bil-adama da 'yan cin fadar albarkacin baki na kasar Masar na cewa Jami'an tsaron kasar sun kame Mutane 237 a jihohi daban-daban na kasar 19 daga ciki 'yan jaridu ne yayin da 40 daga cikin su Mata ne.
Rahoton ya ce a birnin Alkahira an kame mutane 82 sai kuma jihar Aljiza da aka kame mutane 5o, jihar Alsharkiya ita ce jihar ta uku wajen yawan mutanan da aka tsare bayan birnin Alkahira da Jihar Aljiza, inda aka kame Mutane 35.
A Jiya Litinin, daya daga cikin mahalarta zanga-zangar ya rasa ransa bayan da motar mai sulke ta jami'an tsaro a garin Eskandariya ta take shi, wannan bawan A... shine mutum na farko da ya rasa ransa sakamakon zanga-zangar adawar baiwa kasar Saudiya tsibiran Tiran da sanafir.
A daidai lokacin da kasar Masar ke tuni da zagayowar ranar 'yanto da tsibirin Sina a jiya Litinin, Al'ummar kasar a yankuna daban-daban sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da gudirin Shugaba Abdulfatah Alsese na baiwa masarautar Ali sa'oud tsibiran Tiran da sanafir tare da bukatar yin murabus din sa.