Burundi : Gwamnati Na Son Ayi Shawara Kafin Ta Shiga Tattaunawa
(last modified Wed, 27 Apr 2016 16:44:37 GMT )
Apr 27, 2016 16:44 UTC
  • Shugaban kasar Burundi, Pierre N'kurinziza
    Shugaban kasar Burundi, Pierre N'kurinziza

Gwamnatin Burundi ta ce ba zata shiga tattaunawar da ake san ran yi ba tsakanin masu ruwa da tsaki a rikicin da kasar ke fama dashi, mundin ba'a yi shawara da ita ba.

Kakakin fadar gwamnatin kasar Willy Nyamitwe ya bayyana a gidan radiyo kasar cewa yana da kyau a gayyace su a hukumance, sanan su san da suwa zasu tattaunawar tukuna.

Gwamnatin ta ce ba zai yi ba a gayyaci masu tada zaune tsaye ba ko kuma wadanda sukayi yunkurin juyin mulki a tattaunawar ba.

Wannan dai na zuwa ne bayan da masu shiga tsakani na kasa da kasa kan rikicin kasar suka sanar da cewa za'a sake komawa zamen tattaunawar samar da mafita kan rikicin kasar ta Burindia ranar Litinin mai zuwa a birnin Arusha na kasar Tanzaniya.

Duk da takunkunman da kasashen duniya suka kakaba mata, har ye zuwa yanzu gwammatin ta Burunda ta ki amuncewa da zaman tattaunawa da 'yan adawa kasar, ko dai wadanda suke cikin kasar ko kuma wadanda ke gudun hijira.