Priministan Kasar Congo Brazaville Ya Bayyana Sunayin Ministocinsa A Yau Lahadi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4603-priministan_kasar_congo_brazaville_ya_bayyana_sunayin_ministocinsa_a_yau_lahadi
Priministan kasar Congo Brazaville ya bayyana sunayen ministocinsa a yau Lahadi.
(last modified 2018-08-22T11:28:12+00:00 )
May 01, 2016 11:50 UTC
  • Priministan Kasar Congo Brazaville Ya Bayyana Sunayin Ministocinsa A Yau Lahadi

Priministan kasar Congo Brazaville ya bayyana sunayen ministocinsa a yau Lahadi.

Priministan kasar Congo Brazaville ya bayyana sunayen ministocinsa a yau Lahadi. Tashar Radion kasar Faransa ta Kasa da kasa ce bayyana wannan labarin a yau Lahadi, ta kuma kara da cewa majalisar ministocin Kalmon Mowambo sun hada da sabbin fuskoki kuma matasa, a yayinda biyar daga cikinsu tsoffin ministoci ne na gwamnatin da ta shude.

Shugaban kasar ta Congo Brazaville Denis Saso-Ngesu, wanda yayi rantsuwar kama aiki a ranar 16 ga watan Afrilun da ya gabata, ya nada Kalmon Mowambo kan kujerar Priminista ne Jim kadan bayan haka. Kalmon Mowambo ya taba zama ministan kudi a gawamnatin Pascal Lissoumba.