Nijar : Ma'aikatan Kanfanin Hakar Urenium Na Yajin Aiki
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4732-nijar_ma'aikatan_kanfanin_hakar_urenium_na_yajin_aiki
A Jamhuriya NIjar ma'aikatan kanfanin hakar urenium na COMINAK dake yiwa hamshakan kanfanin na Farsansa Areva aiki a arewacin kasar na gudanar da wani yajin aikin na kwanakin uku.
(last modified 2018-08-22T06:58:13+00:00 )
May 03, 2016 12:55 UTC
  • wani wurin hakar urenium a Arlit
    wani wurin hakar urenium a Arlit

A Jamhuriya NIjar ma'aikatan kanfanin hakar urenium na COMINAK dake yiwa hamshakan kanfanin na Farsansa Areva aiki a arewacin kasar na gudanar da wani yajin aikin na kwanakin uku.

Ma'aikatan dai sun fara yajin aiki ne tun daga jiya Litinin domin nuna fishin su akan rashin samun wasu kudaden alawus-alawus da kanfanin yake bayarwa a matsayin wani gebe na riba da yake samu a kowace shekara.

Kanfanin dilancin labaren Reuters ya rawaito cewa yajin aikin ya samu karbuwa sosai daga kungiyar ma'aikatan ta Synamin su 800 koda yake tara daga cikin su sun kaurewa yakin aikin.

Saidai da yake maida martani kan yajin aikin majanan kanfanin na Cominak ya ce yajin aiki baya bisa ka'ida saboda sun cimma yerjejeniya a watan Yuni bara da ma'aikatan cewa kashi 70% na alawus kin shekara data gabata za'a basu, sanan a cike masu sauren daga baya, kuma a cewar sa duk ma'aikatan tuni aka basu wannan kason.

A shekara 2015 data gabata kawai kanfanin na Cominak ya samar da tonne 1.607 na urenium.