Farmakin 'yan sanda kan taron 'Yan jaridu a Masar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4759-farmakin_'yan_sanda_kan_taron_'yan_jaridu_a_masar
Jami'an 'yan sandar Masar Sun aukawa 'yan Jaridu masu zanga-zangar lumana a birnin Alkahira
(last modified 2018-08-22T06:58:13+00:00 )
May 04, 2016 12:41 UTC
  • Farmakin 'yan sanda kan taron 'Yan jaridu a Masar

Jami'an 'yan sandar Masar Sun aukawa 'yan Jaridu masu zanga-zangar lumana a birnin Alkahira

A wannan Laraba, 'yan Jaridun kasar Masar sun gudanar da zanga-zangar Lumana a birnin Alkahira inda suka taro a gaban ofishin kungiyar 'yan jaridun kasar tare da neman Ministan cikin gidan kasar Majdi Abdul-Gafur ya yi murabus.

Daga cikin irin taken da mahalarta zanga-zangar ke rerewa aiki Jarida ba laifi ba ne, sannan kuma suna sukan Shugaban Kasar Afdulfatah Alsese kan kudirin da ya dauka na ganin bayan masu kafafen yada Labarai.

Rahoton ya ce Jami'an 'yan sanda sun kai farmaki kan mahalarta zanga-zangar.

A ranar 1 ga watan Mayu ma Jami'an 'yan sandar na Masar sun kai farmaki kan ofishin kungiyar 'yan jaridun na Masar tare da Kame biyu daga cikin su.

Wannan cin zarafi da ake yiwa 'yan jaridun na Masar ya fuskanci kakkausar suka daga MDD, Kungiyar Tarayyar Turai da wasu kasashen Duniya.

A cewar Babban saktaren kungiyar 'yan jaridun na Masar, ba su taba fuskanta matsin lamba da tsankwama ba kamar na wannan lokaci.