Damuwar Pape Francis kan ci gaba da rikici a kasar Burundi.
Shugaban Cocin Katolika na Duniya ya bayyana damuwarsa kan ci gaba da rikici a kasar Burundi.
Kafar watsa labaran Afirka time ta nakalto Shugaban Cocin katolika Pape Francois Francis na cewa ci gaba da cacar baki da kuma kudirin da Tarayyar Turai ta dauka na kawo karshen rikicin kasar Burundin ya hana gudanar da zama tsakanin gwamnatin da 'yan adawa, kuma hakan babu abinda zai aifar face ci gaba da tashin hanhali a kasar
Pape Francis ya ce ya zuwa yanzu babu wata alama dake nuna cewa za a kawo karshen rikicin, baya ga haka a kwai alamar shakku kan tattaunawar da aka shirya tsakanin bangaren Gwamnati da 'yan adawa ranar 21 ga wannan wata na Mayu da muke ciki a kasar Tanzaniya.
A wata sanarwa da ta fitar a baya bayan nan kungiyar tarayyar Turai ta ce ta dakatar da taimakon da take Baiwa kasar Burundin har sai bangarorin biyu sun amince sun zauna kan tebirin tattaunawa domin fitar da kasar daga yanayin da take ciki na rikicin siyasa, lamarin dake ci gaba da lashe rayukan Mutane.