Ci gaba Da Rikici A kasar Burundi
May 12, 2016 09:13 UTC
Har yanzu kasar Buurndi na fama da rikici.
Tashar telbijin din watsa labaru ta France 24 ta ambato wata majiyar tsaron kasar Burundi na cewa; Wasu mahara da ba a kai ga tantance su ba, sun kashe mutane 3 fararen hula a kudu maso yammacin kasar tare kuma da jikkata wasu da dama.
Shekara daya kenan daga sake zabar shugaba Pierre Nkurunziza, sai dai har yanzu rikicin bai kare ba.
Jam'iyyun siyasa da kuma kungiyoyin fararen hula ne dai su ka nuna kin amincewarsu da sake tsayawa takarar shugaban kasar ta Burundi a zaben Aprilu na 2015.
Baya ga kashe mutane da ake yi, wasu dubban 'yan kasar sun yi hijira zuwa kasar Tanzania, domin samun mafaka.
Tags