Nijar : An Kara Yawan Majalisar Ministoci
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5374-nijar_an_kara_yawan_majalisar_ministoci
A Jamhuriyar Nijar yanzu haka yawan majalisar ministocin kasar ya karu zuwa 41, tun bayan da shugaban kasar ya sanar da sabuwar majalisar ministocinsa mai kunshe da wakilai 38, bayan sake zabensa.
(last modified 2018-08-22T06:58:17+00:00 )
May 19, 2016 06:40 UTC
  • Nijar : An Kara Yawan Majalisar Ministoci

A Jamhuriyar Nijar yanzu haka yawan majalisar ministocin kasar ya karu zuwa 41, tun bayan da shugaban kasar ya sanar da sabuwar majalisar ministocinsa mai kunshe da wakilai 38, bayan sake zabensa.

A ranar Talata ce shugaban kasar Mahamadou Issoufou ya sanya hannu kan wata sabuwar doka, inda ya nada Ahmat Jidoud a matsayin ministan kasafin kudi.

A cen baya dama shugaba Issoufou ya nada wani tsohon jagoran 'yan tawaye Rhissa Ag Boula a matsayin minista a ofishin shugaban kasa, yayin da ya nada Chika Rakiato Bako minista mai kula da raya yankunan karkaka.

Dama kafin hakan yawan ministocin ya hadasa kace-nace ba kadan ba tsakanin al'umma wannan kasar, dake cikin jerin kasashe mafi talauci a duniya.