Kira Domin Kwance Damarar Yaki A Kasar Demokradiyyar Congo.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i538-kira_domin_kwance_damarar_yaki_a_kasar_demokradiyyar_congo.
Sojojin Kasar Demokradiyyar Congo Suna Shirin Kwancewa "yan Tawaye Damarar Yaki A gabacin Kasar.
(last modified 2018-08-22T06:57:47+00:00 )
Feb 09, 2016 15:36 UTC
  • Kira Domin Kwance Damarar Yaki A Kasar Demokradiyyar Congo.

Sojojin Kasar Demokradiyyar Congo Suna Shirin Kwancewa "yan Tawaye Damarar Yaki A gabacin Kasar.

Shafin watsa labarin na African Time, ya ambato majiyar tsaro na cewa; sojojin gwamnatin kasar ta Demokradiyyar Congo sun isa yankin Lubero da ke gundumar Kivo ta Arewa a wani masomin kwace makaman kungiyoyin da su ke cikin gabacin kasar.

Kakakin shirin tabbatar da zaman lafiya a ake kira Sokolo 1 Mak Hazukay ya ce; Shirin na sojojij gwmanati ya zo ne a matsayin wani yunkuri na hana kungiyoyin da su ke dauke da makamai kai farmaki a yankin Miriki da ke arewacin Goma.

A cikin kwanakin bayan nan dai yan tawayen kungiyar yanto da Rawanda da ake kira (FDLR) sun kai wasu munanan hare-hare a yankin na Miriki, wanda ya dauki rayukan mutane 18.

Gabacin kasar Demokradiyyar Congo dai ya zama tunga ta kungiyoyin 'yan tawayen kasashen makwabta.