Shugaban Niger Ya Bayyana Damuwarsa Kan Matsalar Tsaro A Yammacin Afrika
Shugaban kasar Niger ya bayyana cewa; Kasarsa da sauran kasashen yankin yammacin Afrika suna fuskantar barazanar kungiyar ta'addanci ta Boko Haram da a halin yanzu haka kungiyar ta addabi kasashen da suke yankin tafkin Chadi.
A ziyarar aikin da ya fara gudanarwa a kasar Ivory Coast a jiya Alhamis: Shugaban kasar Niger Muhammadu Yusuf ya gana da shugaban kasar Alhasan Watara a birnin Adbijan cibiyar kasuwancin Ivory Coast, inda ganawar bangarorin biyu ta fi mai da hankali kan matsalar tsaro da barazanar ayyukan ta'addanci a yankin yammacin Afrika.
Shugaban kasar Niger Muhammadu Yusuf ya bayyana cewa; Bullar kungiyoyi masu tsaurin ra'ayin addini a yankin yammacin Afrika babbar barazana ce ga kasashen yankin, kuma a halin yanzu haka kasashen suna fuskantar matsalar tsaro saboda ayyukan ta'addancin da kungiyoyin suke aiwatarwa.
Har ila yau shugabannin kasashen biyu sun tattauna batutuwa da dama da suka shafi alakar da ke tsakanin kasashensu tare da jaddada yin aiki tare da nufin bunkasa harkokin ci gaban kasashen da ma sauran kasashen yankin baki daya.