Nuna Damuwar Majalisar Dinkin Duniya Akan Kasar Congo
May 21, 2016 12:32 UTC
Majalisar dinkin duniya ta nuna damuwa akan hare-haren da ake kai wa a gabacin kasar Congo.
A jiya juma'a ne babban magatakardar majalisar dinkin duniya Bon Ki Moon ya bayyana damuwarsa akan hare-haren da sojojin gwamnatin Congo so ke kai wa a gabacin kasar.
Bon Ki Moon wanda ya ke magana ta wayar tarho da shugaban kasar congo Denis Sassou N'Guesso ya nuna damwarsa akan farmakin da jami'an tsaron su ka kai a yanin Pool da ke kudu maso gabcin kasar.
Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniyar ya bukaci da a bai wa kungiyoyin kare hakkin bil'adama damar shiga cikin yankin.
Tags