Tattaunawar Sulhu Akan Rikicin Kasar Burundi
(last modified Sun, 22 May 2016 10:25:17 GMT )
May 22, 2016 10:25 UTC
  • Tattaunawar Sulhu Akan Rikicin Kasar Burundi

Bangarorin gwamnati da na 'yan tawayen kasar Burundi sun ci gaba da tattauanwa a kasar Tanzania.

A jiya asabar ne dai aka bude tattaunawar a tsakanin wakilan gwamnati da kuma na 'yan adawar kasar Burundi a birnin Arusha na kasar Tanzania, domin warware rikicin siyasar kasar.

Kungiyar kasashen gabacin Afirka sun bayyana gamsuwarsu da cewa sake komawa kan teburin tattaunawar da bangarorin na Burundi su ka yi, shi ne kadai hanyar kawo karshen tashin hankalin da kasar ta ke da shi.

Jakadan Tarayyar Turai a kasar Tanzania, Roeland van de Geer da ya gabatar da jawabi a wurin taron, ya kira yi dukkanin bangarorin da su yi matukar kokarinsu wajen ganin sun cimma matsaya.

Burundi dai ta fada cikin rikicin siyasar tun bayan tazarcen da shugaba Pierre Nkurunziza ya yi a shekarar da ta gabata.