An Kashe 'Yan ta'adda Masu Yawa A Masar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5791-an_kashe_'yan_ta'adda_masu_yawa_a_masar
Majiyar Tsaron Masar ta tabbatar da kashe masu dauke da makamai a gabacin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:20+00:00 )
May 26, 2016 07:34 UTC
  • An Kashe 'Yan ta'adda Masu Yawa A Masar

Majiyar Tsaron Masar ta tabbatar da kashe masu dauke da makamai a gabacin kasar.

Kamfanin Dillancin Labarun Kasar Jordan ya nakalto wat amajiyar tsaron kasar na cewa; A yau alhamis ne jami'an tsaron kasar ta Masar su ka kai farmaki a wata mabuya ta 'yan ta'adda a yankin Sheikh Zuwaid da ke birnin Rafah, idan su ka kashe shida daga cikinsu.

Majiyar tsaron ta Kasar masar ta ci gaba da cewa; An kuma sami wasu motoci da babura da 'yan ta'addar su kan yi amfani da su wajen kai harin, kuma tuni an lalata su.

A wani labarin na daban daga garin Rafah, sojojin masar din hudu sun mutu a yayin da su ke kokarin kwance wani bom da aka dasa a jiya laraba.

Yankin Sina ta arewa dai yana fama da matsalolin tsaro saboda tungar da 'yan ta'adda su ka yi a cikinsa.