UEMOA Ta Tallafawa Nijar Kan Shirin Noma
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5866-uemoa_ta_tallafawa_nijar_kan_shirin_noma
Kasar Nijar ta samu gajiyar wani tallafin kungiyar tattalin arziki da kudi ta yammacin Afrika (UEMOA) na fiye da CFA biliyan uku da ya shafi fadin eka 1000 domin bunkasa noma, kiwo da kamun kifi.
(last modified 2018-08-22T06:58:21+00:00 )
May 27, 2016 13:54 UTC
  • UEMOA Ta Tallafawa Nijar Kan Shirin Noma

Kasar Nijar ta samu gajiyar wani tallafin kungiyar tattalin arziki da kudi ta yammacin Afrika (UEMOA) na fiye da CFA biliyan uku da ya shafi fadin eka 1000 domin bunkasa noma, kiwo da kamun kifi.

Shirin na cikin tsarin shiyya game da sauyin yanayi da kungiyar UEMOA da kasashen mambobin kungiyar suke aiwatarwa a halin yanzu.

Manufar shirin ita ce samar da abinci ga al'ummomin kasar da ke cikin halin tagaiyara sakamakon sauyin yanayi.

Yarjejeniyar ta samu sanya hannun ministan kasa na Nijar dake kula da harkokin noma da kiwo, Albade Abouba, da kuma komishinan dake kula da sashen tsaron abinci na UEMOA, Ibrahima Dieme.

A cewar Albade Abouba, rattaba hannu kan wannan yarjejeniya kokarin hukumomin NIjer ne domin nisantar al'ummomin kasar daga yunwa, da tattabar musu da yanayin da ya dace wajen samar da albarkatun noma cikin kasa.

Wannan shirin dai zai shafi jihohin Dosso, Maradi, Tahoua da kuma Tillabery.