Nijar : Sojoji Sun Dakile Harin Boko Haram A Bosso
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5941-nijar_sojoji_sun_dakile_harin_boko_haram_a_bosso
Ma'aikatar tsaro a jamhuriya Nijar ta sanar da dakile wani harin 'yan ta'ada boko haram a garin Bosso dake jihar Diffa a yankin kudu maso gabashin kasar mai iyaka da Najeriya.
(last modified 2018-08-22T06:58:21+00:00 )
May 29, 2016 01:08 UTC
  • Nijar : Sojoji Sun Dakile Harin Boko Haram A Bosso

Ma'aikatar tsaro a jamhuriya Nijar ta sanar da dakile wani harin 'yan ta'ada boko haram a garin Bosso dake jihar Diffa a yankin kudu maso gabashin kasar mai iyaka da Najeriya.

Wata sanarwa da kakakin rundinar sojin kasar, kanal Moustapha Ledrux ya karanto a gidan radiyo na kasar jiya Asabar, ta ce sojojin kasar sun dakile wani harin boko haram tareda kashe gommai da raunana da dama daga cikinsu, a yayin da suka yunkuri kai hari wa sansanin sojin garin na Bosso da yammacin rana juma'a data gabata.

Sanarwar ta kara da cewa an samu tarin makaman yaki daga 'yan ta'adan wadanda suka hada da makaman harba roka kirar (RPG-7) da gurgeti da caja-caja na harsashan bindiga da kuma wayoyin salula.

Saidai a hannu daya sanarwar ta ce akwai wasu sojojin kasar uku da suka raunana a yayin fafatawar.

Tun dai watan Fabariru bara ne, yankin gabashin kasar ta Nijar musamen Bosso da Diffa dake iyaka da Najeriya, ke fuskantar hare-haren kungiyar ta Boko haram, wanda kayo yanzu yayi sanadin mutuwar dariruwan mutane da suka hada da sojoji da fararen hula, tare da cilastawa dubbai tserewa daga gidajensu.

Alkalumen da rundinar sojin Nijar ta fitar sun nuna cewa sama da 'yan ta'ada dubu ne aka kashe ko kuma ake tsare dasu tun dai bayan da kasar ta sa kafar wando guda da kungiyar ta Boko haram.