Nijar : Kwararun Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aiki Na Kwanaki Biyar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6061-nijar_kwararun_likitoci_sun_tsunduma_yajin_aiki_na_kwanaki_biyar
A jamhuriya Nijar yau kwanan biyu kenan da Kwararun likitoci a kasar suka tsunduma cikin wani yajin aiki na kwanaki biyar domin cilastawa gwamnatin kasar biya masu wasu jerin bukatunsu.
(last modified 2018-08-22T06:58:22+00:00 )
May 31, 2016 13:44 UTC
  • Nijar : Kwararun Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aiki Na Kwanaki Biyar

A jamhuriya Nijar yau kwanan biyu kenan da Kwararun likitoci a kasar suka tsunduma cikin wani yajin aiki na kwanaki biyar domin cilastawa gwamnatin kasar biya masu wasu jerin bukatunsu.

Likitocin dai na neman ga gwamnatin kasar data inganta yanayin aikin su da halin da yanayin rayuwarsu.

Abin tuni dai yau kusan shekara guda da rabi da bangarorin biyu ke jayeya akan kara masu wasu kudaden alawus da kuma albashi wanda zaiyi daidai da karatun da sukayi.

Aman a cewar gwamnatin kasar ba zata iya yin fiye da yadda take yi wa likitocin ba a yanzu.

Saidai a cewar Dr Konguizé babban sakataren kungiyar kwararun likitocin zasu ci gaba da wannan kokawa har sai gwamnatin ta biya musu jerin bukatocinsu gabadaya.

Rahotanni daga kasar sun nuna cewa harkoki sun tsaya ci a mayan asibitoci dama kanana da masu zamen kansu a Yamai babban birnin Kasar.