Nijar : Boko Haram Ta Sake Kai Wani Mummunan Hari A Diffa
Rahotanni dake cin karo da juna daga jamhuriya Nijar ne cewa 'yan boko haram sun sake kai wani mumunan hari a garin Bosso dake kusa da yankin tafkin Chadi a iyaka da Najeriya.
Harin dai na yammacin jiya Juma'a a cewar rahotanni ya cilastawa sojojin kasar janyewa daga yankin sa'o'i kadan bayan da maharan suka farbawa garin.
Saidai a cewar ministan tsaro na kasar sojojin sun ja daga ne, kuma bayan hakan sun maida martani, koda yake babu wanda ya gamsu da wannan bayanin.
Abun damuwa dai a nan shi ne dubun al'umma ke rayiwa a wurin.
ko ranar Laraba data gabata ma dai mayakan na boko haram sun farmawa garin na Bosso inda wasu rahotanni ke cewa sun kashe mutane akalla 9 tareda jikkata wani adadi mai yawa.