Al'ummar Nijar Sun Yi Allawadai Da Hare-Haren Boko Haram
Jun 05, 2016 06:45 UTC
Jama'a da dama ne suka fito kan titunan birnin Yamai fadar mulkin Jamhuriyar Nijar domin yin Allawadai da hare-haren ta'addancin da Boko Haram a kasar.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya habarta cewa, masu gangamin da suka hada da kungiyoyin farar hula, 'yan kwadago da kuma wasu 'yan siyasa sun yi ta rera taken yin Allawadai da ayyukan ta'addancin da kungiyar ta Boko Haram take kaddamarwa a kasar, tare da yin kira ga mahukunta da su dauki kwararan matakan kawo karshen wannan kungiya a kasar.
A daren Juma'a da ta gabata ne 'yan ta'addan Boko Haram suka kaddamar da wasu munanan hare-hare a yankin Bosso, inda suka kashe sojojin Nijar 30 da wasu sojojin Najeriya 2, tare da jikkata wasu 67.
Tags