Sama da Mutane 20 ne Suka jikkata sanadiyar tashin gurnaiti a Burundi.
Sanadiyar tashin gurnaiti a wata Anguwa mai yawan jama'a a Bujunbura babbar birnin kasar Burundi, Akalla mutane 26 ne suka jikkata.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ta nakalto mutanan da suka ganewa idanunsu abinda ya wakana na cewa da misalin karfe daya da rabi na kasar, wani Mutum a kan babur ya jefa gurneti tsakanin bainar jama'a a anguwar Buyenzi mai yawan cunkoson jama'a dake birnin Bujunbura, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar mutane 26.
Mista Pierre Nkurikiye kakakin 'yan sanda Burundi ya tabbatar da wannan labari, inda ya ce daga cikin mutanan da suka jikkata a kwai kananen yara guda biyu, sai kuma wata tsohuwa mai yawan shekaru, sannan kuma 9 daga cikin su suna cikin mawuyacin hali.
Tun bayan da shugaba Pierre Nkurinziza ya bayyana shirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasar karo na uku a watan Avrilun shekarar 2015 din da ta gabata,'yan siyasar kasar suka fara cacar baki, lamarin da ya jefa kasar cikin rikici tare da sanadiyar mutuwar mutane da dama.
A wani sabon rahoto da ta fitar Majalisar Dinkin Duniya ta ce daga farkon rikicin kasar ta Burundi, Akalla Mutane 400 ne suka rasa rayukansu.