Nijar : An Fara Zamen Makoki Na Kwanaki Uku
Gwamnatin Nijar ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku domin nuna alhini ga sojoji da kuma al`ummar kasar da suka rasa rayukansu a wani hari da mayakan Boko-haram suka kai garin Bosso, na Jihar Diffa da ke kudu maso gabashin kasar.
Kafin hakan dai gwamnatin kasar ta fitar da wata sanarwa Jiya Litinin dake cewa mutane 26 ne suka mutu a harin na ranar Juma'a, ba 32 ba kamar yadda aka sanar da farko.
Sabbin alkalumen sun nuna cewa sojojin kasar 24 ne suka rasu sai kuma wasu biyu na Najeriya, sannan an hallaka 'yan ta'adan na Boko haram 55.
Sanarwar da kakakin gwamnatin kasar Assoumana Malan Isa ya karanto a gidan talabijib din kasar ta kuma ce an samu sojojin 111 da suka raunana da kuma wata mata fara huaa guda.