Tura Sojojin Tchadi zuwa Kasar Nijer
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6457-tura_sojojin_tchadi_zuwa_kasar_nijer
Kasar Tchadi ta tura Duban Sojoji zuwa Niger
(last modified 2018-08-22T06:58:24+00:00 )
Jun 08, 2016 13:53 UTC
  • Tura Sojojin Tchadi zuwa Kasar Nijer

Kasar Tchadi ta tura Duban Sojoji zuwa Niger

Jaridar Le Figaro ta kasar Faransa ta habarta cewa Majiyar tsaron kasar Tchadi ta sanar a wannan Laraba cewa kasar ta tura sojoji dubu biyu zuwa jumhoriyar Nijer domin kamawa takwarorinsu na Nijer a yakin da su ke yi da kungiyar ta'addancin nan ta boko haram.

Bayan mumunan harin da kungiyar boko haram ta kai garin Bosso dake Jihar Diffa a kudu maso gabashin Jumhoriyyar ta Nijer a ranar Juma'ar da ta gabata, wanda ya yi sanadiyar mutuwar Sojojin kasar 26 da kuma na Tarayyar Najeriya guda biyu, Gwamnatin ta Nijer ta bukaci Magabatan kasar Tchadin da su taimaka musu wajen murkushe mayakan na kungiyar boko haram a kudu masu gabashin kasar.

Majiyar tsaron ta ce tun a ranar litinin da ta gabata ce Dakarun tsaron kasar dauke da manyan makamai suka doshi kasar ta Nijer daga yankunan daban-daban domin dakile duk wani yunkurin harin ta'addanci na mayakan Boko Haram.

Tun daga Watan Favrayun shekarar 2015 kasar ta Nijer ta fara fuskantar harin ta'addanci na Kungiyar Boko Haram.